19 Afirilu 2022 - 19:53
Iran Tana Da Kyakkyawar Mahanga Game Da Kasar Afghanistan

Ministan harkokin wajen kasar iran Amir Abdollahiyan ya yi zantawa ta wayar tarho Amir Khan Muttaki wanda shi ne ministan harkokin wajen kasar Afghanistan na riko a gwamnatin da Taliban ta kafa inda ya bayyana cewa iran tana da kyakkawar mahanga kuma mai kima game da kasar Afghanistan, domin iran ta karbi bakunci miliyoyin yan Afghanistan a kasarta fiye da shekaru 40 da suka gabata kuma suna cin gajiyar muhimman abubuwan mure rayuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har ila yau ya nuna takaicinsa game da mummunan parfagandar karya da makiya suke yadawa a kafafen sadarwa na zamani domin bata kyakkyawar alaka dake tsakanin kasashen biyu

Yace muna tsammanin gwamnatin rikon kwaryar kasart ta Afghanistan za ta samar da hanyoyin yin aiki tare tsakaninta da kasar iran wajen bada tsaro ga jami’an diplomasiyar kasar iran dake Kabul , da kuma kula da ikokin kasashen da kuma hana shige da fice ba tare da izini ba, da kuma aiki da nauyin day a ratawa awunysa bisa yarjeniyoyin da aka cimma tsakani

Anasa bangaren minsitan harkokin wajen na rika na Afghanistan ya nuna damuwarsa matuka game da hadarin da ya faru a baya bayan nan na hari da aka kai kan ofishin Diplomasiyar iran dake birnin Kabul da Herat , kana ya bada tabbacin samar da cikakken tsaro ga dukkan kadarori da jami’an diplomsiyar iran dake kasar.

342/